Littafi Mai Tsarki

Luk 22:51-63 Littafi Mai Tsarki (HAU)

51. Yesu ya amsa ya ce, “Ku ƙyale su haka.” Sai ya taɓa kunnen bawan, ya warkar da shi.

52. Yesu kuma ya ce wa waɗanda suka tasar masa, wato, manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali da shugabannin jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake, kamar masu kama ɗan fashi?

53. Sa'ad da nake tare da ku kowace rana a cikin Haikali, ba ku miƙa hannu garin ku kama ni ba. Amma wannan lokacinku ne da na ikon duhu.”

54. Sai suka kama shi, suka tafi da shi, suka kai shi cikin gidan babban firist. Bitrus kuwa yana biye daga nesa nesa.

55. Da suka hura wuta a tsakar gida suka zazzauna, Bitrus ma ya zauna a cikinsu.

56. Sai wata baranya ta gan shi zaune a hasken wuta, ta zura masa ido, ta ce, “Ai, mutumin nan ma, tare da shi yake.”

57. Amma ya musa ya ce, “Ke, ban ma san shi ba.”

58. Bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, sai wani ya gan shi, ya ce, “Kai ma, ai, ɗayansu ne.” Amma Bitrus ya ce, “Ya mutum, ba haka ba ne.”

59. Bayan wajen sa'a guda sai wani ya nace, ya ce, “Ba shakka mutumin nan ma tare da shi yake, don Bagalile ne.”

60. Amma Bitrus ya ce, “Haba, ban ma san abin da kake faɗa ba.” Nan take, kafin ya rufe baki, sai zakara ya yi cara.

61. Sai Ubangiji ya juya ya dubi Bitrus. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Ubangiji ya faɗa masa cewa, “A yau ma kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

62. Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

63. Sai mutanen da suke riƙe da Yesu suka yi ta masa ba'a, suna dūkansa.