Littafi Mai Tsarki

Fit 8:18-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Masu sihiri suka ƙokarta su sa kwarkwata ta bayyana ta wurin sihirinsu, amma ba su iya ba. Kwarkwata kuma ta yayyaɓe 'yan adam da dabbobi.

19. Sai masu sihiri suka ce wa Fir'auna, “Ai, wannan aikin Allah ne.” Amma zuciyar Fir'auna ta taurare, har da bai kasa kunne ga Musa da Haruna ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

20. Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe ka sami Fir'auna a daidai lokacin da ya fita za shi rafi, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.

21. In kuwa ka ƙi sakin jama'ata, sai in koro maka ƙudaje, da kai da fādawanka, da jama'arka, da gidajen Masarawa, har ma duk da ƙasa inda suke takawa.

22. A wannan rana fa zan keɓe ƙasar Goshen inda jama'ata suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, ta haka ne za ka sani ni Ubangiji ina nan a duniya.

23. Zan sa iyaka tsakanin jama'ata da jama'arka. Gobe ne wannan mu'ujiza za ta auku.”’

24. Haka kuwa Ubangiji ya aikata. Ƙudaje masu yawa suka shiga gidan Fir'auna, da gidan fādawansa, da ko'ina a ƙasar Masar. Ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje.

25. Sa'an nan Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce, “Tafi, ku yi wa Allahnku hadaya a ƙasan nan.”

26. Amma Musa ya ce, “Ba zai kyautu a yi haka ba, gama irin dabbobin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu hadaya da su, haramu ne ga Masarawa. Idan fa muka miƙa hadaya da waɗannan dabbobi da suke haramu a idon Masarawa za su jajjefe mu da duwatsu.

27. Za mu yi tafiya kwana uku a jeji kafin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu kamar yadda ya umarce mu.”