Littafi Mai Tsarki

Fit 38:18-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. An yi wa labulen ƙofar farfajiya ado na ɗinki da na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin. Tsawonsa kamu ashirin, tsayinsa kamu biyar daidai da labulen farfajiya.

19. An yi dirkokin labulen guda huɗu, da kwasfan dirkoki guda huɗu da tagulla, amma da azurfa aka yi maratayan dirkokin. An dalaye kawunansu da maɗauransu da azurfa.

20. An yi turakun alfarwa ta sujada da na farfajiya duka da tagulla.

21. Wannan shi ne lissafin abubuwan da aka yi alfarwa ta sujada da su, yadda aka lasafta bisa ga umarnin Musa domin aikin Lawiyawa a ƙarƙashin jagorar Itamar, ɗan Haruna firist.

22. Sai Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza, ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa.

23. Tare da shi kuma ga Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan, gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin.

24. Dukan zinariya da aka yi aikace-aikacen da ita na alfarwa ta sujada sadaka ce talanti ashirin da tara ne da shekel ɗari bakwai da talatin bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.

25. Azurfar da aka samu daga ƙidayar taron jama'a talanti ɗari ne, da shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba'in da biyar (1,775) bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.

26. Kowane mutum da aka ƙidaya ya ba da rabin shekel. Duk mai shekara ashirin ko fi an ƙidaya shi, aka sami maza dubu ɗari shida da dubu uku da ɗari biyar da hamsin (603,550).

27. An mori azurfa talanti ɗari don yin kwasfa na alfarwa, da kwasfa na labule. An yi kwasfa ɗari da azurfa talanti ɗari, wato kwasfa ɗaya talanti ɗaya ke nan.

28. An yi maratayan dirkoki da azurfa shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba'in da biyar (1,775), sa'an nan an dalaye kawunansu, an kuma yi musu maɗaurai.

29. Tagullar da aka bayar kuwa, talanti saba'in da shekel dubu biyu da ɗari huɗu (2,400).

30. Da tagullar ce ya yi kwasfan ƙofar alfarwa ta sujada, da bagade, da ragarsa, da dukan kayayyakin bagaden.

31. Da tagullar kuma aka yi kwasfan farfajiya, da kwasfan ƙofar farfajiya, da dukan turakun alfarwar da na farfajiyar.