Littafi Mai Tsarki

Luk 23:28-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Amma Yesu ya juya gare su, ya ce, “Ya ku matan Urushalima, ku bar yi mini kuka, sai dai ku yi wa kanku da kuma 'ya'yanku,

29. don lokaci na zuwa da za su ce, ‘Albarka tā tabbata ga matan da suke bakararru, waɗanda ba su taɓa haihuwa ba, waɗanda kuma ba a taɓa shan mamansu ba.’

30. Sa'an nan ne za su fara ce wa manyan duwatsu, ‘Ku faɗo a kanmu,’ su kuma ce da tsaunuka, ‘Ku binne mu.’

31. In fa irin abubuwan nan suna faruwa ga ɗanye, yaya zai zama ga ƙeƙasasshe?”

32. Waɗansu mutum biyu kuma masu laifi, aka kai su a kashe su tare da shi.

33. Da suka isa wurin da ake ce da shi Ƙoƙwan Kai, nan suka gicciye shi, da kuma masu laifin nan, ɗaya a damansa, ɗaya a hagun.

34. Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri'a a kansu.

35. Mutane da suke tsaitsaye, suna kallo. Shugabanni kuma suka yi masa ba'a, suka ce, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa mana, in shi ne Almasihu na Allah zaɓaɓɓensa!”

36. Soja kuma suka yi masa ba'a, suka matso, suka miƙa masa ruwan tsami,

37. suna cewa, “In kai ne Sarkin Yahudawa, to, ka cece kanka mana!”

38. Sama da shi kuma aka yi wani rubutu cewa, “Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.”