Littafi Mai Tsarki

Fit 12:16-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. A kan rana ta fari za ku yi tsattsarkan taro, haka kuma za ku yi a rana ta bakwai. A cikin waɗannan ranaku ba za a yi kowane aiki ba, sai na abin da kowa zai ci.

17. Za ku kiyaye idin abinci marar yisti, gama a wannan rana na fitar da rundunarku daga ƙasar Masar. Ku kiyaye wannan rana dukan zamananku. Wannan farilla ce ta har abada.

18. Za ku ci abinci marar yisti da maraice a kan rana ta goma sha huɗu ga wata na fari, har zuwa rana ta ashirin da ɗaya ga watan da maraice.

19. Amma kada a iske yisti a gidajenku har kwana bakwai, gama idan wani ya ci abin da aka sa wa yisti za a fitar da shi daga cikin taron jama'ar Isra'ila, ko shi baƙo ne ko kuwa haifaffen ƙasar.

20. Dukan abin da yake da yisti ba za ku ci shi ba, wato sai abinci marar yisti ne kaɗai za ku ci a dukan gidajenku.”

21. Musa ya kirayi dattawan Isra'ila duka, ya ce musu, “Gaggauta, ku zaɓa wa kanku ɗan tunkiya ko akuya bisa ga iyalanku, ku yanka domin Idin Ƙetarewa.

22. Ku ɗauki tuntun ezob, ku tsoma cikin jinin da yake a kasko, ku yarfa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada kowa ya fita daga gidansa sai da safe.

23. Gama Ubangiji zai ratsa don ya kashe Masarawa, sa'ad da ya ga jinin a bisa kan ƙofar, da dogaran ƙofa duka biyu sai ya wuce ƙofar, ba zai bar mai hallakarwa ya shiga gidanku, ya kashe ku ba.

24. Za ku kiyaye waɗannan ƙa'idodi, ku riƙe su farilla, ku da 'ya'yanku har abada.

25. Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku kamar yadda ya alkawarta, wajibi ne ku kiyaye wannan farilla.

26. Sa'ad da 'ya'yanku suka tambaye ku, ‘Ina ma'anar wannan farilla?’

27. Za ku ce, ‘Hadaya ce ta Idin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra'ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.”’ Sai jama'ar suka durƙusa suka yi sujada.