Littafi Mai Tsarki

Luk 5:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Domin shi da waɗanda suke tare da shi duka, mamaki ya kama su saboda kifin nan da suka janyo,

10. haka ma Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi, abokan sabgar Bitrus. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.”

11. Da suka kawo jiragensu gaci, suka bar kome duka suka bi shi.

12. Wata rana Yesu na ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa ya zo. Da ya ga Yesu ya fāɗi a gabansa, ya roƙe shi ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda kana da ikon tsarkake ni.”

13. Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take sai kuturtar ta rabu da shi.

14. Yesu ya kwaɓe shi kada ya gaya wa kowa, ya ce, “Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi hadaya saboda tsarkakewarka, domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”

15. Amma duk da haka labarinsa sai ƙara yaɗuwa yake yi, har taro masu yawan gaske suka yi ta zuwa domin su saurare shi, a kuma warkar da su daga rashin lafiyarsu.

16. Amma shi, sai ya riƙa keɓanta a wuraren da ba kowa, yana addu'a.

17. Wata rana na koyarwa, waɗansu Farisiyawa kuwa da masanan Attaura da suka fito daga kowane gari na ƙasar Galili, da na ƙasar Yahudiya, daga kuma Urushalima, suna nan a zaune. Ikon Ubangiji na warkarwa kuwa yana nan.

18. Sai ga waɗansu mutane ɗauke da wani shanyayye a kan shimfiɗa, suna ƙoƙari su shigar da shi su ajiye shi a gaban Yesu.

19. Da suka kasa samun hanyar shigar da shi saboda taro, suka hau a kan soron, suka zura shi ta tsakanin rufin soron duk da shimfiɗarsa, suka ajiye shi a tsakiyar jama'a a gaban Yesu.

20. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce, “Malam, an gafarta maka zunubanka.”