Littafi Mai Tsarki

Luk 17:5-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai manzanni suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya.”

6. Ubangiji kuwa ya ce, “Da kuna da bangaskiya, ko da misalin ƙwayar mastad, da za ku ce wa wannan durumi, ‘Ka ciru, ka dasu cikin teku,’ sai kuwa ya bi umarninku.”

7. “Misali, wane ne a cikinku in yana da bawa mai yi masa noma ko kiwon tumaki, da zarar ya dawo daga jeji, zai ce masa, ‘Maza, zo ka zauna, ka ci abinci’?

8. Ashe, ba ce masa zai yi, ‘Shirya mini jibi, ka kuma yi ɗamara, ka yi mini hidima, har in gama ci da sha, daga baya kai kuma ka ci ka sha,’ ba?

9. Yā gode wa bawan nan don ya bi umarni?

10. Haka ku ma, in kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, ‘Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da yake wajibinmu kurum.’ ”

11. Wata rana yana tafiya Urushalima, sai ya bi iyakar ƙasar Samariya da Galili.

12. Yana shiga wani ƙauye ke nan, sai waɗansu kutare maza guda goma suka tarye shi, suna tsaye daga nesa.

13. Sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Maigida Yesu, ka ji tausayinmu,”

14. Da ya gan su, ya ce musu, “Ku je wurin firistoci su gan ku.” Suna tafiya ke nan, sai suka tsarkaka.

15. Ɗayansu kuma da ganin an warkar da shi, ya komo, yana ta ɗaukaka Allah da murya mai ƙarfi,

16. ya fāɗi a gaban Yesu, yana gode masa. Shi kuwa Basamariye ne.

17. Yesu ya amsa ya ce, “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina taran?

18. Ashe, ba wanda aka samu ya komo ya ɗaukaka Allah, sai baƙon nan kaɗai?”

19. Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”

20. Da Farisiyawa suka tambaye shi lokacin bayyanar Mulkin Allah, ya amsa musu ya ce, “Ai, bayyanar Mulkin Allah ba ganinta ake yi da ido ba.

21. Ba kuwa za a ce, ‘A! Ga shi nan,’ ko kuwa, ‘Ga shi can,’ ba. Ai, Mulkin Allah a tsakaninku yake.”

22. Ya kuma ce wa almajiran, “Lokaci na zuwa da za ku yi begen ganin rana ɗaya daga cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba.

23. Za su ce muku, ‘A! ga shi nan,’ ko kuwa, ‘Ga shi can!’ Kada ku je, kada ku bi su.

24. Kamar yadda walƙiya take wulgawa walai, daga wannan bangon duniya zuwa wancan, haka ma, Ɗan Mutum zai zama a ranar bayyanarsa.

25. Amma lalle sai ya sha wuya iri iri tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ƙi shi.