Littafi Mai Tsarki

Luk 13:6-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sai ya ba su misalin nan ya ce, “Wani mutum yana da ɓaure a garkar inabinsa. Sai ya zo neman 'ya'ya, amma bai samu ba.

7. Sai ya ce wa mai kula da garkar, ‘Ka ga, yau shekara uku ke nan nake zuwa neman 'ya'yan wannan ɓaure, amma ba na samu. A sare shi. Ƙaƙa zai tsare wuri a banza?’

8. Sai ya amsa masa ya ce, ‘Ubangijina, bar shi dai bana ma, in yi masa kaftu, in zuba masa taki.

9. In ya yi 'ya'ya, to, in kuwa bai yi ba, sai a sare.’ ”

10. Wata rana yana koyarwa a wata majami'a ran Asabar,

11. sai ga wata mace wadda inna ta shanye tun shekara goma sha takwas, duk ta tanƙware, ko kaɗan ba ta iya miƙewa.

12. Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, “Uwargida, an raba ki da rashin lafiyarki!”

13. Sai ya ɗora mata hannu, nan take ta miƙe, ta kuma ɗaukaka Allah.

14. Amma shugaban majami'a ya ji haushi, don Yesu ya warkar ran Asabar. Sai ya ce wa jama'a, “Akwai ranaku har shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo mana a ranakun nan a warkar da ku, ba ran Asabar ba.”

15. Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe, kowannenku ba ya kwance takarkarinsa ko jakinsa a turke, ya kai shi banruwa ran Asabar?

16. Ashe, bai kamata matar nan 'yar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya ɗaure, yau shekara goma sha takwas, a kwance ta daga wannan ƙuƙumi a ran Asabar ba?”

17. Da ya faɗi haka, sai duk abokan adawarsa suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwan al'ajabi da yake yi.

18. Sai Yesu ya ce, “Da me Mulkin Allah yake kama? Da me kuma zan kwatanta shi?

19. Kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa, ta kuma girma ta zama itace, har tsuntsaye suka yi sheƙarsu a rassanta.”

20. Ya sāke cewa, “Da me zan kwatanta Mulkin Allah?

21. Kamar yisti yake wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗa da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya gama da yistin.”