Littafi Mai Tsarki

Luk 13:21-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Kamar yisti yake wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗa da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya gama da yistin.”

22. Sai ya ɗauki hanyarsa ta zuwa birane da ƙauyuka, yana koyarwa, yana dosar Urushalima.

23. Sai wani ya ce masa, “Ya Ubangiji, waɗanda za su sami ceto kam, kaɗan ne?” Sai ya ce musu,

24. “Ku yi famar shiga ta ƙunƙuntar ƙofa. Don ina gaya muku, mutane da yawa za su nemi shiga, amma ba su iya ba.

25. In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe ƙofa, kun kuma fara tsayawa daga waje, kuna ƙwanƙwasa ƙofar, kuna cewa, ‘Ya Ubangiji, buɗe mana,’ sai ya amsa muku ya ce, ‘Ku kam, ban san daga inda kuke ba.’

26. Sa'an nan za ku fara cewa, ‘Ai, mun ci mun sha a gabanka, har ka koyar a kan titi-titinmu.’

27. Shi kuwa sai ya ce, ‘Ina dai gaya muku, ku kam, ban san daga inda kuke ba. Ku tafi daga wurina, dukanku ku masu aikata mugunta!’

28. Sa'ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, da dukan annabawa a Mulkin Allah, ku kuwa ana korarku, a nan ne za ku yi kuka da cizon baki.

29. Za a zo daga gabas da yamma, kudu da arewa, a zauna cin abinci a Mulkin Allah.

30. Ga shi fa, waɗansu da suke na ƙarshe za su zama na farko, waɗansu kuwa da suke na farko za su koma na ƙarshe.”

31. Nan take waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ai, sai ka tashi, ka fita daga nan, gama Hirudus yana son kashe ka.”

32. Sai ya ce musu, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, ‘Ka ga, yau ina fitar da aljannu, ina warkarwa, gobe ma haka, a rana ta uku kuwa zan gama aikina.

33. Duk da haka, lalle ne in ci gaba da tafiyata yau da gobe, da kuma jibi, don kuwa bai dace a kashe annabi ba, in ba a Urushalima ba.’

34. “Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko gare ku! Sau nawa ne ina so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta a cikin fikafikanta, amma kun ƙi!

35. Ga shi, an bar muku gidanku a yashe! ina kuwa gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”