Littafi Mai Tsarki

Luk 13:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Nan take waɗansu da suke a wurin suka ba shi labarin Galilawan da Bilatus ya sa aka kashe, har jininsu ya gauraya da na yankan da suka yi na hadaya.

2. Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galilawa sun fi duk sauran Galilawa zunubi ne, don sun sha wannan azaba?

3. Ina gaya muku ba haka ba ne! In kuwa ba ku tuba ba, duk za ku halaka kamarsu.

4. Ko kuwa goma sha takwas ɗin nan da hasumiya ta faɗo a kansu, a Siluwam, ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?

5. Ina gaya muku ba haka ba ne! In kuwa ba ku tuba ba, duk za ku hallaka kamarsu.”

6. Sai ya ba su misalin nan ya ce, “Wani mutum yana da ɓaure a garkar inabinsa. Sai ya zo neman 'ya'ya, amma bai samu ba.

7. Sai ya ce wa mai kula da garkar, ‘Ka ga, yau shekara uku ke nan nake zuwa neman 'ya'yan wannan ɓaure, amma ba na samu. A sare shi. Ƙaƙa zai tsare wuri a banza?’

8. Sai ya amsa masa ya ce, ‘Ubangijina, bar shi dai bana ma, in yi masa kaftu, in zuba masa taki.

9. In ya yi 'ya'ya, to, in kuwa bai yi ba, sai a sare.’ ”

10. Wata rana yana koyarwa a wata majami'a ran Asabar,

11. sai ga wata mace wadda inna ta shanye tun shekara goma sha takwas, duk ta tanƙware, ko kaɗan ba ta iya miƙewa.

12. Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, “Uwargida, an raba ki da rashin lafiyarki!”

13. Sai ya ɗora mata hannu, nan take ta miƙe, ta kuma ɗaukaka Allah.