Littafi Mai Tsarki

Luk 11:30-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Wato, kamar yadda Yunusa ya zama alama ga mutanen Nineba, haka kuma, Ɗan Mutum zai zamar wa zamanin nan.

31. A Ranar Shari'a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan ta kā da su. Don ta zo ne daga bangon duniya tă ga hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan.

32. A Ranar Shari'a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan su kā da su. Don sun tuba saboda wa'azin Yunusa. To, ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.”

33. “Ba mai kunna fitila ya ɓoye ta a rami, ko ya rufe ta da masaki. A'a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken.

34. Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka zai cika da haske. In kuwa idonka da lahani, sai jikinka ya cika da duhu.

35. Saboda haka, sai ka lura ko hasken da yake a gare ka duhu ne.

36. In kuwa duk jikinka ya cika da haske, ba inda ke da duhu, ai, duk sai ya haskaka gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila take haskaka maka.”

37. Yesu yana magana, sai wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Ya shiga cin abincin.

38. Sai Bafarisiyen ya yi mamakin ganin yadda Yesu zai ci abinci ba da fara wanke hannu ba.