Littafi Mai Tsarki

Luk 10:28-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Yesu ya ce masa, “Ka amsa daidai. Ka riƙa yin haka, za ka rayu.”

29. Shi kuwa mutumin, don yana son baratar da kansa, ya ce wa Yesu, “To, wane ne ɗan'uwa nawa?”

30. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ne ya tashi daga Urushalima za shi Yariko. Sai 'yan fashi suka fāɗa shi, suka tuɓe shi, suka yi masa mugun dūka, suka tafi suka bar shi rai ga Allah.

31. Daga nan ya zamana wani firist ya biyo ta wannan hanya. Da ya gan shi sai ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa.

32. Haka kuma wani Balawe, da ya iso wurin ya gan shi, shi ma ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa.

33. Ana nan sai hanya ta kawo wani Basamariye inda yake. Da ya gan shi, sai tausayi ya kama shi,

34. ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa, yana zuba musu mai da ruwan inabi. Sa'an nan ya ɗora shi a kan dabbarsa, ya kai shi masauki, ya yi ta jiyyarsa.

35. Kashegari ya ɗebo dinari biyu ya ba maigidan, ya ce, ‘Ka yi jiyyarsa, duk kuma abin da ka ɓatar bayan wannan, in na dawo sai in biya ka.’

36. To, a cikin ukun nan, wa kake tsammani ya zama ɗan'uwa ga wanda 'yan fashin suka faɗa wa?”

37. Sai ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Sai Yesu ya ce masa, “Kai ma, ka je ka riƙa yin haka.”

38. Suna tafiya, sai ya shiga wani ƙauye, wata mace kuma mai suna Marta ta sauke da shi a gidanta.

39. Tana kuwa da 'yar'uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana sauraron magana tasa.

40. Marta kuwa yawan hidimomi ya ɗauke mata hankali, sai ta je gunsa, ta ce, “Ya Ubangiji, ba ka kula ba, 'yar'uwata ta bar ni ina hidima ni kaɗai? Gaya mata ta taimake ni mana.”