Littafi Mai Tsarki

L. Mah 1:16-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Zuriyar Bakene, surukin Musa kuwa suka fita tare da mutanen Yahuza daga birnin dabino, wato Yariko, suka tafi jejin Yahuda da take a Negeb kudu da Arad. A can suka zauna tare da Amalekawa.

17. Yahuza kuwa da ɗan'uwansa, Saminu, suka tafi suka bugi Kan'aniyawan da suke zaune a Zefat. Suka la'anta birnin, suka hallaka shi, suka sāke wa birnin suna Horma, wato hallakarwa.

18. Yahuza kuma ya ci Gaza da karkararta, da Ashkelon da karkararta, da Ekron da karkararta.

19. Ubangiji kuwa yana tare da Yahuza, ya mallaki ƙasar tuddai, amma bai iya korar waɗanda suke zaune a fili ba, domin suna da karusan ƙarfe.

20. Aka ba Kalibu Hebron kamar yadda Musa ya faɗa. Shi kuwa ya kori 'ya'yan Anak, maza, su uku, a can.

21. Amma mutanen Biliyaminu ba su kori Yebusiyawan da suke zaune a Urushalima ba domin haka Yebusiyawa suka yi zamansu tare da mutanen Biliyaminu a Urushalima har wa yau.

22. Jama'ar kabilar Yusufu kuwa suka haura don su yaƙi Betel, Ubangiji kuwa yana tare da su.

23. Suka aika a leƙi asirin Betel wadda a dā ake kira Luz.

24. Sai 'yan leƙen asirin ƙasar suka ga wani mutum yana fitowa daga cikin birnin, suka ce masa, “Muna roƙonka ka nuna mana hanyar shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.”

25. Ya kuwa nuna musu, suka shiga suka kashe dukan mutanen birnin, amma suka bar mutumin da iyalinsa duka.