Littafi Mai Tsarki

L. Fir 13:12-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Idan kuturtar ta faso a fatar jikin mutum har ta rufe fatar jikin mutumin daga kai zuwa ƙafa a iyakar ganin firist,

13. firist ɗin zai duba shi, in kuturtar ta rufe jikin duka, zai hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne daga cutar, gama kuturtar ta rikiɗa, ta yi fari fat, don haka ya tsarkaka.

14. Amma a ranar da aka ga sabon miki a jikinsa zai zama marar tsarki.

15. Sai firist ya dudduba sabon mikin ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, sabon miki fa marar tsarki ne, gama kuturta ce.

16. Idan kuma sabon mikin ya juya, ya rikiɗa ya zama fari, zai tafi wurin firist.

17. Firist ɗin zai dudduba shi, idan cutar ta rikiɗa ta zama fara, sai firist ya hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne, gama ya tsarkaka.

18. Amma idan akwai wanda yake da ƙurjin da ya warke,

19. idan kuma akwai tabo jaja-jaja, da fari-farin tabo, sai a nuna wa firist.

20. Firist zai dudduba shi, idan zurfin kumburin ko tabon rikiɗa fari, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce ta faso a ƙurjin.

21. Amma idan firist ya dudduba shi ya ga gashin wurin bai yi fari ba, zurfin ƙurjin kuma bai zarce fatar ba, amma ya dushe, sai firist ɗin ya kulle shi kwana bakwai.

22. Amma idan ƙurjin ya bazu a fatar jikin, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, kuturta ce.