Littafi Mai Tsarki

Fit 34:18-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. “Sai ku kiyaye idin abinci marar yisti har kwana bakwai a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a watan Abib kuka fito Masar. A lokacin za ku ci abinci marar yisti kamar yadda na umarce ku.

19. “Kowane ɗan farin mutum, ko na dabba nawa ne, duk da 'ya'yan farin dabbobinku, wato ɗan farin saniya da na tunkiya.

20. Ɗan farin jaki kuwa za ku fansa da ɗan rago, in kuwa ba za ku fansa da ɗan rago ba, sai ku karya wuyansa. Za ku fanshi kowane ɗan fari. Kada a sami wanda ya zo gabana hannu wofi.

21. “Cikin kwana shida za ku yi aiki, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, ko lokacin noma ne, ko lokacin girbi sai ku huta.

22. “Ku kuma kiyaye idin mako, wato idin girbin nunan fari na alkama, da idin gama tattara amfanin gonaki a ƙarshen shekara.

23. “Sau uku cikin shekara mazajenku duka za su hallara a gabana, ni Ubangiji Allah na Isra'ila.

24. Gama zan kori al'ummai daga gabanku, in fāɗaɗa kan iyakarku. Ba wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokatan nan uku na shekara da kukan hallara a gaban Ubangiji Allahnku.

25. “Ba za ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti ba, kada kuma a bar hadaya ta Idin Ƙetarewa ta kwana.

26. “Sai ku kawo nunan farin amfanin gonarku a cikin gidan Ubangiji Allahnku.“Kada ku dafa ɗan akuya da madarar uwarsa.”

27. Ubangiji ya kuma ce wa Musa, “Rubuta waɗannan kalmomi, gama daidai suke da kalmomin alkawarin da suke tsakanina, da kai, da Isra'ila.”

28. Musa kuwa yana tare da Ubangiji yini arba'in da dare arba'in, bai ci ba, bai sha ba. Sai ya rubuta kalmomin alkawarin a kan allunan, wato dokokin nan goma.

29. Sa'ad da Musa ya sauko daga Dutsen Sina'i da alluna biyu na alkawarin a hannunsa, ashe, bai sani ba, amma fuskarsa tana annuri saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji.

30. Sa'ad da Haruna da dukan jama'ar Isra'ila suka ga fuskar Musa tana annuri, suka ji tsoro su kusace shi.

31. Sai Musa ya kirawo Haruna tare da shugabannin jama'ar duka, suka zo wurinsa, shi kuwa ya yi magana da su.

32. Daga nan jama'ar Isra'ila duka suka matsa kusa, Musa kuwa ya ba su dukan dokoki waɗanda Ubangiji ya ba shi a bisa Dutsen Sina'i.

33. Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa.

34. Amma duk lokacin da ya je gaban Ubangiji domin ya yi magana da shi, sai ya kware lulluɓin, har lokacin da ya fito. Idan ya fito, sai ya faɗa wa jama'ar Isra'ila abin da aka umarce shi.

35. Jama'ar Isra'ila kuwa sukan ga fuskar Musa tana annuri. Sa'an nan Musa ya sāke lulluɓe fuskarsa, har lokacin da ya shiga don ya yi magana da Ubangiji.