Littafi Mai Tsarki

Esta 9:22-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Su ne ranakun da Yahudawa suka sami kuɓuta daga abokan gābansu. A wannan wata ne kuma baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama hutawa. Sai su maishe su ranakun biki da farin ciki, da aika wa juna da abinci, da kuma ba da kyautai ga matalauta.

23. Sai Yahudawa suka ɗauka su yi kamar yadda suka fara, da kuma yadda Mordekai ya rubuta musu.

24. Haman Ba'agage, ɗan Hammedata, maƙiyin dukan Yahudawa, ya ƙulla wa Yahudawa makirci don ya hallaka su. Ya jefa Fur, wato kuri'a don ya hallaka su.

25. Amma da Esta ta zo wurin sarki, sai sarki ya ba da umarni a rubuce,cewa mugun makircin nan da Haman ya shirya wa Yahudawa ya koma a kansa. Shi da 'ya'yansa maza aka rataye su a bisa gumagumai.

26. Saboda haka suka sa wa ranakun nan suna Furim, wanda asalinsu daga Fur ne, wato kuri'a. Domin haka dukan abin da aka rubuta a wannan takarda, da abin da suka gani a wannan al'amari, da abin da ya same su,

27. sai Yahudawa suka ga wajibi ne a gare su, da zuriyarsu, da waɗanda ka tare da su, su kiyaye ranaku biyu ɗin nan ba fashi kowace shekara, bisa ga abin da aka rubuta.

28. Za a tuna da ranakun nan, a kiyaye su a kowane zamani, da kowane iyali, da lardi, da birni. Ranakun Furim ɗin nan, Yahudawa ba za su daina tunawa da su ba, zuriyarsu kuma ba za ta daina tunawa da su ba.

29. Sa'an nan sarauniya Esta 'yar Abihail, da Mordekai Bayahude, ta ba da cikakken iko a rubuce don ta tabbatar da takardan nan ta biyu game da Furim.

30. Aka aika da takardun zuwa ga dukan Yahudawa da suke a lardi ɗari da ashirin da bakwai na mulkin Ahasurus, da kalmomin salama da na gaskiya,

31. da cewa a kiyaye ranakun Furim a lokacinsu, kamar yadda Mordekai Bayahude, da sarauniya Esta, suka umarci Yahudawa, kamar yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu lokacin tunawa da azuminsu da baƙin cikinsu.