Littafi Mai Tsarki

Esta 7:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sarki da Haman kuwa suka tafi wurin Esta, gun liyafa.

2. A rana ta biyu, sa'ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya sāke ce wa Esta, “Mece ce bukatarki, sarauniya Esta? Za a yi miki. Mene ne roƙonki? Za a ba ki, ko da rabin mulkina ne.”

3. Sai Esta ta ce, “Ya sarki, idan na sami tagomashi a wurinka, idan kuma sarki ya yarda, bukatata ita ce a bar ni da raina, roƙona kuma shi ne a bar mutanena.

4. Gama an sayar da mu, ni da mutanena, don a hallaka mu, a karkashe, a ƙarasa mu. Da a ce an sayar da mu mu zama bayi, mata da maza, da na yi shiru, gama ba za a kwatanta wahalarmu da hasarar da sarki zai sha ba.”

5. Sarki Ahasurus ya ce wa sarauniya Esta, “Wane ne shi, ina yake, wanda zai yi karambanin yin wannan?”

6. Esta ta ce, “Haman ne, magabci, maƙiyi, mugu!”Sai tsoro ya kama Haman a gaban sarki da sarauniya.

7. Sarki kuwa ya tashi da fushi, ya tafi lambun fāda. Amma Haman ya tsaya don ya roƙi sarauniya Esta ta ceci ransa, gama ya ga sarki yana niyyar hukunta shi.