Littafi Mai Tsarki

Mar 7:3-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Domin Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci sai sun wanke hannu sarai tukuna, saboda bin al'adun shugabanninsu.

4. In sun komo daga kasuwa kuwa, ba sa cin abinci sai sun yi wanka tukuna. Akwai kuma waɗansu al'adu da yawa da suka gada suke kiyayewa, kamar su wankin ƙore, da tuluna, da daruna.

5. Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka tambaye shi, “Don me almajiranka ba sa bin al'adun shugabanni, sai su riƙa cin abinci da hannuwa marasa tsarki?”

6. Sai ya ce musu, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, munafukai! Yadda yake a rubuce cewa,‘Al'umman nan a baka kawai suke girmama ni,Amma a zuci nesa suke da ni.

7. A banza suke bauta mini,Domin ƙa'idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.’

8. Kuna yar da umarnin Allah, kuna riƙe da al'adun mutane.”

9. Sai ya ce musu, “Lalle kun iya yar da umarnin Allah don ku bi al'adunku!

10. Domin Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ da kuma, ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa, sai lalle a kashe shi.’

11. Amma ku kukan ce, ‘In mutum ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni ya zama Korban,” ’ (wato an sadaukar),

12. shi ke nan fa, ba saura ku bar shi ya yi wa ubansa ko uwa tasa aikin kome.

13. Ta haka kuke banzanta Maganar Allah ta wajen al'adunku na gargajiya. Kun kuwa cika yin irin waɗannan abubuwa.”

14. Sai ya sāke kiran jama'a, yă ce musu, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimta.

15. Ba abin da yake shiga mutum daga waje yă ƙazanta shi, sai abin da yake fita, yake ƙazanta shi. [

16. Duk mai kunnen ji, yă ji.]”

17. Bayan rabuwarsa da taron, da ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi ma'anar misalin.