Littafi Mai Tsarki

Luk 9:22-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Ya ce, “Lalle ne Ɗan mutum yă sha wuya iri iri, shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.”

23. Sai ya ce wa dukansu, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, yă bi ni.

24. Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, tattalinsa ya yi.

25. Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a kan hasarar ransa, ko a bakin ransa?

26. Duk wanda sai ya ji kunyar shaida ni da maganata, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi sa'ad da ya zo da ɗaukaka tasa, da kuma ɗaukakar Uba, da ta mala'iku tsarkaka.

27. Amma hakika ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Mulkin Allah.”

28. Bayan misalin kwana takwas da yin maganan nan, Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, ya hau wani dutse domin yin addu'a.

29. Yana yin addu'a, sai kama tasa ta sāke, tufafinsa kuma suka yi fari fat, har suna ɗaukar ido.

30. Sai ga mutum biyu na magana da shi, wato Musa da Iliya.

31. Sun bayyana da ɗaukaka, suna zancen ƙaura tasa ne, wadda yake gabannin yi a Urushalima.

32. Sai kuma Bitrus da waɗanda suke tare da shi, barci ya cika musu ido, amma da suka farka suka ga ɗaukakarsa, da kuma mutum biyun nan tsaye tare da shi.

33. Mutanen nan na rabuwa da shi ke nan, sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Maigida, ya kyautu da muke nan wurin. Mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” Bai ma san abin da yake faɗa ba.

34. Yana faɗar haka sai wani gajimare ya zo ya rufe su. Da kuma gajimaren ya lulluɓe su suka tsorata.

35. Sai aka ji wata murya daga cikin gajimaren, tana cewa, “Wannan shi ne Ɗana zaɓanɓɓena. Ku saurare shi!”

36. Bayan muryar ta yi magana, aka ga Yesu shi kaɗai. Suka yi shiru. A kwanakin nan kuwa ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.

37. Kashegari da suka gangaro daga kan dutsen, wani babban taro ya tarye shi.

38. Sai ga wani daga cikin taron ya yi kira, ya ce, “Malam, ina roƙonka ka dubi ɗana da idon rahama, shi ne ke nan gare ni.

39. Ga shi, aljani yakan hau shi, yakan yi ihu ba zato ba tsammani. Aljanin yakan buge shi, jikinsa yana rawa, har bakinsa yana kumfa. Ba ya barinsa sai ya kukkuje shi ƙwarai.

40. Na kuwa roƙi almajiranka su fitar da shi, amma sun kasa.”