Littafi Mai Tsarki

Luk 8:48-56 Littafi Mai Tsarki (HAU)

48. Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”

49. Yana cikin magana, sai ga wani ya zo daga gidan shugaban majami'ar, ya ce, “Ai, 'yarka ta rasu. Kada ka ƙara wahalar da Malamin.”

50. Amma da Yesu ya ji haka, ya amsa ya ce wa shugaban majami'ar, “Kada ka ji tsoro. Ka ba da gaskiya kawai, za ta kuwa warke.”

51. Da ya isa gidan bai yarda kowa ya shiga tare da shi ba, sai Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da kuma uban yarinyar da uwa tata,

52. Duk kuwa ana ta kuka da kururuwa saboda ita. Amma Yesu ya ce, “Ku daina kuka. Ai, ba matacciya take ba, barci take yi.”

53. Sai suka yi masa dariyar raini, don sun sani ta mutu.

54. Shi kuwa sai ya riƙe hannunta, ya ta da murya ya ce, “Yarinya, ki tashi.”

55. Ruhunta kuwa ya dawo, nan take ta tashi. Sai ya yi umarni a ba ta abinci.

56. Iyayenta suka yi mamaki. Amma ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da ya faru.