Littafi Mai Tsarki

Luk 23:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Da Bilatus ya ji haka, ya tambaya ko mutumin nan Bagalile ne.

7. Da ya ji Yesu a ƙarƙashin mulkin Hirudus yake, sai ya aika da shi wurin Hirudus, don shi ma yana Urushalima a lokacin.

8. Da Hirudus ya ga Yesu, ya yi murna ƙwarai, saboda tun da daɗewa yake son ganinsa, don ya riga ya ji labarinsa, yana kuma fata ya ga wata mu'ujiza da Yesu zai yi.

9. Sai ya yi ta masa tambayoyi da yawa, amma bai amsa masa da kome ba.

10. Manyan firistoci da malaman Attaura na nan a tsaitsaye, suna tsananta kai ƙararrakinsa ainun.

11. Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba'a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus.

12. A ran nan sai Hirudus da Bilatus suka yi sulhu, don dā abokan gāba ne.

13. Bilatus ya tara manyan firistoci da shugabanni da kuma jama'a,

14. ya ce masu, “Kun kawo mini mutumin nan a kan, wai yana ɓad da jama'a, na kuwa tuhunce shi a gabanku, amma ban same shi da wani laifi a ƙararrakinsa da kuka kawo ba.

15. Hirudus ma bai samu ba, don ya komo mana da shi. Ga shi kuwa, bai yi wani abu da ya cancanci kisa ba.

16. Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”[

17. A lokacin idi kuwa lalle ne ya sakar musu ɗaurarre guda.]