Littafi Mai Tsarki

Luk 23:5-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai suka fara matsa masa lamba, suna cewa, “Yana ta da hankalin jama'a, yana koyarwa a dukan ƙasar Yahudiya, tun daga ƙasar Galili har zuwa nan.”

6. Da Bilatus ya ji haka, ya tambaya ko mutumin nan Bagalile ne.

7. Da ya ji Yesu a ƙarƙashin mulkin Hirudus yake, sai ya aika da shi wurin Hirudus, don shi ma yana Urushalima a lokacin.

8. Da Hirudus ya ga Yesu, ya yi murna ƙwarai, saboda tun da daɗewa yake son ganinsa, don ya riga ya ji labarinsa, yana kuma fata ya ga wata mu'ujiza da Yesu zai yi.

9. Sai ya yi ta masa tambayoyi da yawa, amma bai amsa masa da kome ba.

10. Manyan firistoci da malaman Attaura na nan a tsaitsaye, suna tsananta kai ƙararrakinsa ainun.

11. Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba'a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus.

12. A ran nan sai Hirudus da Bilatus suka yi sulhu, don dā abokan gāba ne.

13. Bilatus ya tara manyan firistoci da shugabanni da kuma jama'a,

14. ya ce masu, “Kun kawo mini mutumin nan a kan, wai yana ɓad da jama'a, na kuwa tuhunce shi a gabanku, amma ban same shi da wani laifi a ƙararrakinsa da kuka kawo ba.

15. Hirudus ma bai samu ba, don ya komo mana da shi. Ga shi kuwa, bai yi wani abu da ya cancanci kisa ba.

16. Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”[

17. A lokacin idi kuwa lalle ne ya sakar musu ɗaurarre guda.]

18. Amma duk suka ɗauki ihu gaba ɗaya, suna cewa, “A yi da wannan ɗin, a sakar mana Barabbas!”

19. (Barabbas shi ne wani mutum da aka jefa a kurkuku, saboda wani tawayen da aka yi a birni, da kuma kisankai.)

20. Sai Bilatus ya sāke yi musu magana, don yana so ya saki Yesu.

21. Amma suka yi ta ƙwala ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”