Littafi Mai Tsarki

Luk 16:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya kuma ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki da yake da wakili. Sai aka sari wakilin a wurinsa a kan yana fallasar masa da dukiya.

2. Sai ya kira shi ya ce masa, ‘Labarin me nake ji naka? Kawo lissafin wakilcinka, don ba sauran ka zama wakilina.’

3. Sai wakilin ya ce a ransa, ‘Ƙaƙa zan yi, da yake maigida zai karɓe wakilci daga hannuna? Ga shi, ba ni da ƙarfin noma, in yi roƙo kuwa, ina jin kunya.

4. Yauwa! Na san abin da zan yi, don in an fisshe ni daga wakilcin, mutane su karɓe ni a gidajensu.’

5. Sai ya kira mabartan maigidansa da ɗaya ɗaya, ya ce wa na farko, ‘Nawa maigida yake bin ka?’

6. Ya ce, ‘Garwa ɗari ta mai.’ Sai ya ce masa, ‘Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubutu hamsin,’

7. Ya kuma ce wa wani, ‘Kai fa, nawa ake binka?’ Sai ya ce, ‘Buhu ɗari na alkama.’ Ya ce masa, ‘Ga takardarka, ka rubuta tamanin.’