Littafi Mai Tsarki

Luk 13:27-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Shi kuwa sai ya ce, ‘Ina dai gaya muku, ku kam, ban san daga inda kuke ba. Ku tafi daga wurina, dukanku ku masu aikata mugunta!’

28. Sa'ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, da dukan annabawa a Mulkin Allah, ku kuwa ana korarku, a nan ne za ku yi kuka da cizon baki.

29. Za a zo daga gabas da yamma, kudu da arewa, a zauna cin abinci a Mulkin Allah.

30. Ga shi fa, waɗansu da suke na ƙarshe za su zama na farko, waɗansu kuwa da suke na farko za su koma na ƙarshe.”

31. Nan take waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ai, sai ka tashi, ka fita daga nan, gama Hirudus yana son kashe ka.”

32. Sai ya ce musu, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, ‘Ka ga, yau ina fitar da aljannu, ina warkarwa, gobe ma haka, a rana ta uku kuwa zan gama aikina.

33. Duk da haka, lalle ne in ci gaba da tafiyata yau da gobe, da kuma jibi, don kuwa bai dace a kashe annabi ba, in ba a Urushalima ba.’

34. “Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko gare ku! Sau nawa ne ina so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta a cikin fikafikanta, amma kun ƙi!