Littafi Mai Tsarki

L. Mah 5:13-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'an nan amintattu sun zo wurin shugabanninsu,Jama'ar Ubangiji suka zo wurina a shirye domin yaƙi.

14. Daga Ifrraimu mutane suka gangaro zuwa kwari,Bayan kabilar Biliyaminu da mutanenta.Daga Makir shugabannin sojoji suka zo,Daga Zabaluna kuma jarumawa suka gangaro.

15. Shugabannin Issaka suna tare da Debora,Hakika, Issaka ya zo, Barak kuma ya zo,Suka bi bayansu zuwa kwari.Amma kabilar Ra'ubainu ta rarrabu,Ba su shawarta su zo ba.

16. Don me suka tsaya daga baya tare da tumaki?Don su saurari makiyaya na kiran garkuna?Hakika kabilar Ra'ubainu ta rarrabu,Ba su shawarta su zo ba.

17. Kabilar Gad suna tsaya a gabashin Urdun,Kabilar Dan kuma ta tsaya a wuraren kiwo.Kabilar Ashiru ta zauna a bakin teku,Sun zauna a gefen teku.

18. Amma mutanen Zabaluna da na NaftaliSuka kasai da ransu a bakin dāga.

19. Sarakuna suka zo, suka yi yaƙi a Ta'anak,A rafin Magiddo.Sarakunan Kan'ana suka yi yaƙi,Amma ba su kwashe azurfa ba.

20. Daga sama, taurari suka yi yaƙi,Suna gilmawa a sararin samaSuka yi yaƙi da Sisera.

21. Ambaliyar Kishon ta kwashe su,Wato tsohon Kogin Kishon.Zan yi gaba, in yi gaba da ƙarfi!

22. Sa'an nan dawakai sun yi ta rishiSuna ƙwaƙular ƙasa da kofatansu.

23. Mala'ikan Ubangiji ya ce,“Ka la'anta Meroz,Ka la'anta mazauna cikinta sosai,Gama ba su kawo wa Ubangiji gudunmawa ba,Su zo su yi yaƙi kamar sojoji dominsa.”

24. Wadda ta fi kowa sa'a daga cikin mata, sai Yayel,Matar Eber, Bakene,Wadda ta fi kowa sa'a daga cikin matan da suke a alfarwai.

25. Sisera ya roƙi ruwan sha,Sai ta ba shi madara,Ta kawo masa kindirmo a kyakkyawar ƙwarya.

26. Ta ɗauki turken alfarwa a hannunta,Ta riƙe guduma a guda hannun,Ta bugi Sisera, kansa ya fashe,Ta kwankwatse kansa, ya ragargaje.