Littafi Mai Tsarki

L. Mah 2:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. A duk sa'ad da suka tafi yaƙi sai Ubangiji ya yi gāba da su kamar dai yadda ya faɗa. Saboda haka suka shiga wahala ƙwarai.

16. Sa'an nan Ubangiji ya naɗa musu mahukunta masu ƙarfi da suka cece su daga waɗanda suka washe su.

17. Duk da haka ba su kasa kunne ga mahukuntan ba. Suka yi wa Ubangiji ha'inci, suka yi wa waɗansu alloli sujada. Kakanninsu sun bi umarnin Ubangiji amma wannan tsara nan da nan suka bar yin haka ɗin.

18. Sa'ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan taimake shi, ya kuwa cece su daga abokan gāba dukan kwanakin mahukuncin. Gama Ubangiji ya ji ƙansu saboda nishinsu, da zaluncin da ake yi musu.

19. Amma idan mahukuncin ya rasu, sai su sāke kaucewa, su yi zunubi fiye da na kakanninsu. Suna bin gumaka, suna bauta musu, suna kuma yi musu sujada, ba su daina mugayen ayyukansu na rashin aminci da taurin zuciya ba.

20. Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa ya ce, “Saboda al'umman nan ta ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu, ba su yi biyayya da maganata ba,

21. don haka daga nan gaba ba zan ƙara kore musu wata al'umma daga cikin al'umman da Joshuwa ya rage kafin rasuwarsa ba.