Littafi Mai Tsarki

L. Fir 8:22-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Musa ya kawo ɗayan ragon keɓewa, sai Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon.

23. Musa kuwa ya yanka shi, ya ɗibi jinin, ya sa a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun dama, da babban yatsa na ƙafar dama.

24. Sai aka kawo 'ya'yan Haruna, maza, Musa kuma ya sa jinin a leɓatun kunnensu na dama, da manyan yatsotsi na hannuwansu na dama, da manyan yatsotsin ƙafafu na dama. Sa'an nan ya yayyafa jinin kewaye da bagaden.

25. Ya kuma ɗauki kitsen, da wutsiya mai kitse, da dukan kitsen da yake bisa kayan ciki, da matsarmama da ƙodoji biyu da kitsensu, da cinyar dama.

26. Daga cikin kwandon abinci marar yistin da yake a gaban Ubangiji, ya ɗauki waina guda marar yisti, da waina guda da aka yi da mai, da ƙosai guda. Sai ya ɗibiya su a bisa kitsen da cinyar dama.

27. Ya sa waɗannan abubuwa duka a tafin hannuwan Haruna da na 'ya'yansa maza, ya miƙa abubuwan nan domin hadayar kaɗawa ga Ubangiji.

28. Sa'an nan ya karɓe su daga tafin hannuwansu, ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden don hadayar keɓewa, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

29. Ya kuma ɗauki ƙirjin, ya kaɗa shi don hadayar kaɗawa ga Ubangiji. Wannan shi ne rabon Musa daga cikin ragon keɓewar, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.