Littafi Mai Tsarki

L. Fir 13:10-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Firist kuwa ya dudduba shi, in akwai kumburi a fatar jikin mutum wanda ya rikiɗar da gashin wurin ya zama fari, in kuma akwai sabon miki a kumburin,

11. to, kuturta ce da ta daɗe a fatar jikinsa. Firist kuwa zai hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba za a kulle shi ba, gama ya tabbata marar tsarki ne.

12. Idan kuturtar ta faso a fatar jikin mutum har ta rufe fatar jikin mutumin daga kai zuwa ƙafa a iyakar ganin firist,

13. firist ɗin zai duba shi, in kuturtar ta rufe jikin duka, zai hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne daga cutar, gama kuturtar ta rikiɗa, ta yi fari fat, don haka ya tsarkaka.

14. Amma a ranar da aka ga sabon miki a jikinsa zai zama marar tsarki.

15. Sai firist ya dudduba sabon mikin ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, sabon miki fa marar tsarki ne, gama kuturta ce.

16. Idan kuma sabon mikin ya juya, ya rikiɗa ya zama fari, zai tafi wurin firist.

17. Firist ɗin zai dudduba shi, idan cutar ta rikiɗa ta zama fara, sai firist ya hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne, gama ya tsarkaka.

18. Amma idan akwai wanda yake da ƙurjin da ya warke,

19. idan kuma akwai tabo jaja-jaja, da fari-farin tabo, sai a nuna wa firist.