Littafi Mai Tsarki

L. Fir 1:13-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa'an nan firist ya miƙa duka, ya ƙone a bisa bagaden, gama hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

14. Idan kuma hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji daga cikin tsuntsaye ne, sai ya kawo kurciyoyi, ko 'yan tattabarai.

15. Firist ɗin zai kawo tsuntsun a bagaden, ya murɗe wuyan tsuntsun, sa'an nan ya ƙone kan a bisa bagaden. Za a tsiyaye jini a gefen bagaden.

16. Amma zai ɗauki kururun da gashin ya zubar da su a gefen bagaden a wajen gabas a wurin zuba toka.

17. Zai tsaga shi biyu a tsaka, amma ba zai raba shi ba. Firist ɗin zai ɗibiya shi a bisa itacen da yake bisa bagaden, ya ƙone shi, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.