Littafi Mai Tsarki

Fit 7:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, zan maishe ka kamar Allah ga Fir'auna. Ɗan'uwanka, Haruna kuwa, zai zama manzonka.

2. Kai za ka faɗa wa Haruna, ɗan'uwanka, dukan abin da na umarce ka, shi kuwa zai faɗa wa Fir'auna ya bar Isra'ilawa su fita ƙasa tasa.

3. Amma zan taurare zuciyar Fir'auna don in aikata alamu da mu'ujizai cikin ƙasar Masar.

4. Amma Fir'auna ba zai kasa kunne gare ku ba, don haka zan miƙa hannuna a bisa Masar, zan fitar da rundunar jama'ata, wato Isra'ilawa, daga ƙasar Masar ta wurin hukuntaina masu iko.

5. Masarawa kuma za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na miƙa hannuna gāba da Masar, don in fito da Isra'ilawa daga tsakiyarsu.”

6. Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarce su.

7. Musa yana da shekara tamanin, Haruna kuwa yana da shekara tamanin da uku sa'ad da suka yi magana da Fir'auna.

8. Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

9. “Idan Fir'auna ya ce muku, ‘Aikata waɗansu al'ajabai don ku nuna isarku,’ sai ka faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa, ya jefa shi ƙasa a gaban Fir'auna. Sandan kuwa zai zama maciji.”

10. Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir'auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa a gaban Fir'auna. Da sandan ya fāɗi, sai ya zama maciji.

11. Fir'auna kuwa ya kirawo shahararrun malamai, da masu sihiri, su kuma su yi haka ta wurin sihirinsu na Masarawa.

12. Kowannensu ya jefa sandansa ƙasa, sai sandunan suka zama macizai. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu.

13. Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

14. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir'auna yana da taurin zuciya, ga shi, ya ƙi sakin jama'ar.

15. Ka tafi wurinsa da safe daidai lokacin da ya fita zai tafi Kogin Nilu. Ka jira don ka sadu da shi a bakin Nilu. Ka kuma ɗauki sandan nan wanda ya juye ya zama maciji.

16. Za ka faɗa wa Fir'auna cewa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya aike ni gare ka da cewa ka saki jama'ar Ubangiji domin su yi masa hidima a jeji. Amma ga shi, har yanzu ba ka yi biyayya ba.