Littafi Mai Tsarki

Fit 6:3-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Na bayyana ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a kan ni Allah Maɗaukaki ne, amma sunan nan nawa, Yahweh, ban sanasshe su ba.

4. Na kuma yi musu alkawari zan ba su ƙasar Kan'ana, inda suka yi zaman baƙunci.

5. Yanzu na ji nishin Isra'ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuwa tuna da alkawarina.

6. Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ni Ubangiji zan 'yantar da ku daga wulakancin nan da Masarawa suke yi muku. Zan kuɓutar da ku daga bautar Masarawa. Da ƙarfi zan aikata hukuntaina masu iko don in cece ku.

7. Zan tallafe ku, ku zama jama'ata, ni kuwa in zama Allahnku. A sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya 'yanto ku daga wulakancin Masarawa.

8. Sa'an nan zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse zan bai wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Zan ba ku ita ta zama mallakarku. Ni ne Ubangiji.”’

9. Sai Musa ya faɗa wa Isra'ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne gare shi ba, saboda ɓacin rai da tsananin bauta.

10. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

11. “Tafi gaban Fir'auna, Sarkin Masar, ka faɗa masa ya bar Isra'ilawa su fita ƙasa tasa.”

12. Amma Musa ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Duba, tun da yake Isra'ilawa ba su kasa kunne gare ni ba, yaya Fir'auna zai kasa kunne gare ni, ni mutum mai nauyin baki?”

13. Ubangiji kuma ya yi magana da Musa da Haruna, su tafi wurin Isra'ilawa da wurin Fir'auna, Sarkin Masar, su ba su umarni, su kuma fito da Isra'ilawa daga cikin ƙasar Masar.

14. Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, ɗan farin Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ra'ubainu.

15. 'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan Bakan'aniya, waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu.

16. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Lawi bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari. Lawi ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai.

17. 'Ya'yan Gershon, maza kuwa, su ne Libni, da Shimai bisa ga iyalansu.

18. 'Ya'ya maza na Kohat kuwa, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel. Kohat ya rayu shekara ɗari da talatin da uku.

19. 'Ya'ya maza na Merari, su ne Mali, da Mushi. Waɗannan su ne kabilar Lawi bisa ga zuriyarsu.