Littafi Mai Tsarki

Fit 38:7-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai ya zura sandunan cikin ƙawane na gyaffan bagaden don ɗaukarsa. Ya yi bagaden da itace sa'an nan ya robe cikinsa.

8. Ya yi daron wanka da tagulla, da gammonsa na tagulla, daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.

9. Ya kuma yi farfajiya. Ya yi labulenta na gefen kudu da lallausan zaren lilin, tsawonsu kamu ɗari ne.

10. Da tagulla aka yi dirkokinsa ashirin, da kwasfan dirkoki guda ashirin, amma da azurfa aka yi maratayan dirkoki da maɗaurai.

11. Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne. An yi dirkokinsa guda ashirin da kwasfansu ashirin da tagulla, amma an yi maratayan dirkoki da maɗaurai da azurfa.

12. Labule na gefen yamma kamu hamsin ne, dirkokinsa kuwa guda goma ne, da kwasfansu guda goma. An yi maratayan dirkoki, da maɗaurai da azurfa.

13. Tsawon gefen gabas kamu hamsin ne.

14. Labule na gefe ɗaya na ƙofar, kamu goma sha biyar ne, da dirkokinsu guda uku da kwasfan dirkoki guda uku.

15. Akwai kuma labule mai kamu goma sha biyar a gefe biyu na ƙofar farfajiyar. Labulen yana da dirkoki guda uku da kwasfan dirkoki guda uku.

16. Duk labulen da yake kewaye da farfajiya an yi shi da lallausan zaren lilin.

17. An yi kwasfan dirkoki duka da tagulla, amma maratayan dirkoki da maɗauransu an yi su da azurfa. An dalaye kawunansu da azurfa. Dirkokin farfajiya duka suna da maɗaurai na azurfa.

18. An yi wa labulen ƙofar farfajiya ado na ɗinki da na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin. Tsawonsa kamu ashirin, tsayinsa kamu biyar daidai da labulen farfajiya.

19. An yi dirkokin labulen guda huɗu, da kwasfan dirkoki guda huɗu da tagulla, amma da azurfa aka yi maratayan dirkokin. An dalaye kawunansu da maɗauransu da azurfa.