Littafi Mai Tsarki

Fit 24:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Suka ga Allah na Isra'ila. Wurin da yake ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama.

11. Amma Ubangiji bai yi wa dattawan Isra'ila wani abu ba, ko da yake suka ga zatin Allah. Su kuma suka ci suka sha a gaban Allah.

12. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka hawo zuwa wurina a bisa dutsen, ka zauna har in ba ka allunan dutse da yake da dokoki da farillan da na rubuta don a koya musu.”

13. Sai Musa ya tashi, shi da baransa Joshuwa, suka tafi, suka hau dutsen Allah.

14. Ya ce wa dattawan, “Ku dakata a nan har mu komo wurinku. Haruna da Hur suna tare da ku, in wani yana da wata damuwa, sai ya je wurinsu.” Sa'an nan Musa ya hau bisa dutsen.

15. Da hawan Musa bisa dutsen, girgije ya rufe kan dutsen.

16. Ɗaukakar Ubangiji kuma ta zauna bisa Dutsen Sina'i. Girgijen ya lulluɓe dutsen har kwana shida, a rana ta bakwai kuwa Ubangiji ya kira Musa daga cikin girgijen.

17. Isra'ilawa suka ga ɗaukakar Ubangiji kamar wuta mai cinyewa a bisa ƙwanƙolin dutsen.

18. Sai Musa ya shiga girgijen, ya hau bisa dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba'in da dare arba'in.