Littafi Mai Tsarki

Fit 2:15-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Da Fir'auna ya ji, sai ya nema ya kashe Musa. Amma Musa ya gudu daga gaban Fir'auna, ya tafi, ya zauna a ƙasar Madayana. Da ya kai, sai ya zauna a bakin wata rijiya.

16. Ana nan waɗansu 'yan mata bakwai, 'ya'yan firist na Madayana suka zo su cika komaye da ruwa domin su shayar da garken mahaifinsu.

17. Sai makiyaya suka zo, suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su, ya kuma shayar da garkensu.

18. Lokacin da suka koma wurin mahaifinsu, Reyuwel, wato Yetro, ya ce musu, “Yaya aka yi yau, kuka komo da sauri haka?”

19. Sai suka ce, “Wani Bamasare ne ya cece mu daga hannun makiyaya, har ya ɗebo ruwa, ya shayar da garkenmu.”

20. Reyuwel kuwa ya ce wa 'ya'yansa mata, “A ina yake? Me ya sa ba ku zo da shi ba? Ku kirawo shi, ya zo, ya ci abinci.”

21. Musa kuwa ya yarda ya zauna tare da Reyuwel. Sai ya aurar wa Musa da 'yarsa Ziffora.

22. Ita kuwa ta haifa masa ɗa, ya raɗa masa suna Gershom, gama ya ce, “Baƙo ne ni, a baƙuwar ƙasa.”