Littafi Mai Tsarki

Fit 12:28-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Isra'ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.

29. Da tsakar dare sai Ubangiji ya karkashe dukan 'ya'yan fari maza a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir'auna, wato magajinsa, har zuwa ɗan farin ɗan sarka da yake a kurkuku, har da dukan 'ya'yan fari maza na dabbobi.

30. Da dare Fir'auna ya tashi, shi da dukan fādawansa, da dukan Masarawa, suka yi kuka mai tsanani a Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba.

31. Sai Fir'auna ya sa aka kirawo masa Musa da Haruna da daren, ya ce musu, “Tashi, ku da jama'arku, ku fita daga cikin jama'ata. Tafi, ku bauta wa Ubangiji kamar yadda kuka ce.

32. Kwashi garkunanku na tumaki da awaki, da na shanu, ku yi tafiyarku kamar yadda kuka ce, amma ku sa mini albarka.”

33. Masarawa suka iza mutanen su gaggauta, su fita ƙasar, gama suka ce, “Ƙarewa za mu yi idan ba ku tafi ba.”

34. Sai jama'ar suka ɗauki ƙullun da ba a sa masa yisti ba, da ƙorensu na aikin ƙullun, suka ƙunshe a mayafansu, suka saɓa a kafaɗunsu.

35. Isra'ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa musu, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi.

36. Ubangiji ya sa jama'a su yi farin jini a wurin Masarawa, saboda haka Masarawa suka ba su abin da suka roƙa. Ta haka suka washe Masarawa.