Littafi Mai Tsarki

Fit 12:21-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Musa ya kirayi dattawan Isra'ila duka, ya ce musu, “Gaggauta, ku zaɓa wa kanku ɗan tunkiya ko akuya bisa ga iyalanku, ku yanka domin Idin Ƙetarewa.

22. Ku ɗauki tuntun ezob, ku tsoma cikin jinin da yake a kasko, ku yarfa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada kowa ya fita daga gidansa sai da safe.

23. Gama Ubangiji zai ratsa don ya kashe Masarawa, sa'ad da ya ga jinin a bisa kan ƙofar, da dogaran ƙofa duka biyu sai ya wuce ƙofar, ba zai bar mai hallakarwa ya shiga gidanku, ya kashe ku ba.

24. Za ku kiyaye waɗannan ƙa'idodi, ku riƙe su farilla, ku da 'ya'yanku har abada.

25. Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku kamar yadda ya alkawarta, wajibi ne ku kiyaye wannan farilla.

26. Sa'ad da 'ya'yanku suka tambaye ku, ‘Ina ma'anar wannan farilla?’

27. Za ku ce, ‘Hadaya ce ta Idin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra'ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.”’ Sai jama'ar suka durƙusa suka yi sujada.

28. Isra'ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.

29. Da tsakar dare sai Ubangiji ya karkashe dukan 'ya'yan fari maza a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir'auna, wato magajinsa, har zuwa ɗan farin ɗan sarka da yake a kurkuku, har da dukan 'ya'yan fari maza na dabbobi.