Littafi Mai Tsarki

Fit 1:13-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Suka kuma tilasta wa Isra'ilawa su yi ta aiki mai tsanani.

14. Suka baƙanta musu rai da aiki mai tsanani na kwaɓa, da yin tubali, da kowane irin aiki a saura. A cikin ayyukansu duka suka tsananta musu.

15. Sarkin Masar ya ce wa ungozomar Ibraniyawa, Shifra da Fu'a,

16. “Sa'ad da kuke yi wa matan Ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durƙushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai.”

17. Amma da yake ungozomar masu tsoron Allah ne, ba su yi yadda Sarkin Masar ya umarce su ba, amma suka bar 'ya'ya maza da rai.