Littafi Mai Tsarki

A.m. 7:38-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Shi ne kuma wanda yake a cikin Ikkilisiyar nan a jeji tare da mala'ikan da ya yi masa magana a Dutsen Sinai, tare da kakanninmu kuma. Shi ne kuma ya karɓo rayayyiyar magana domin ya kawo mana.

39. Amma kakanninmu suka ƙi yi masa biyayya, suka ture shi, zuciya tasu ta koma ƙasar Masar.

40. Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana gumakan da za su yi mana jagaba, don Musan nan kam, da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya auku a gare shi ba.’

41. A lokacin nan suka ƙera ɗan maraƙi, suka yanka wa gunkin nan hadaya, suka riƙa farin ciki da aikin da suka yi da hannunsu.

42. Saboda haka Allah ya juya musu baya, ya sallame su ga bautar taurari, yadda yake a rubuce a littafin annabawa cewa,‘Ya ku jama'ar Isra'ila,Ni ne kuka yanka wa dabbobi, kuka miƙa wa hadaya,Har shekara arba'in a cikin jeji?

43. Ai, yawo kuka yi da alfarwar Molek,Da surar tauraron gunki Ramfan,Wato surorin nan da kuka ƙera don ku yi musu sujada.Ni kuwa zan kawar da ku a can bayan Babila.’

44. “Dā kakanninmu suna da alfarwar shaida a jeji, irin wadda mai maganar nan da Musa ya umarta a yi, daidai fasalin da ya gani.

45. Alfarwan nan ita ce kakanninmu suka gāda, suka kuma kawo ƙasar nan a zamanin Joshuwa, bayan sun mallake ƙasar al'umman da Allah ya kora a gaban idonsu. Alfarwan nan kuwa tana nan har ya zuwa zamanin Dawuda,