Littafi Mai Tsarki

Mar 11:4-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai suka tafi, suka tarar da aholakin a ɗaure a ƙofar gida a bakin hanya, suka kwance shi.

5. Sai waɗanda suke tsaitsaye a gun suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?”

6. Suka faɗa musu abin da Yesu ya ce. Su kuwa suka ƙyale su suka tafi.

7. Suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfiɗa mayafansu a kai, ya hau.

8. Sai mutane da yawa suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka baza ganyen da suka kakkaryo a saura.

9. Da na gaba da na baya suka riƙa sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji!

10. Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na ubanmu Dawuda! Hosanna ga Allah!”

11. Sai ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Da dai ya dudduba kome, da yake magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyun nan.

12. Kashegari da suka tashi daga Betanya, ya ji yunwa.

13. Da ya hango wani itacen ɓaure mai ganye kore shar, sai ya je ya ga ko ya sami 'ya'ya. Da ya isa wurinsa bai ga kome ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan ɓaure ba ne.

14. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada kowa ya ƙara cin 'ya'yanka har abada!” Almajiransa kuwa suna ji.

15. Suka iso Urushalima. Ya shiga Haikalin ya fara korar masu saye da sayarwa daga ciki, ya kuma birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai,

16. ya kuma hana kowa ratsa Haikalin ɗauke da wani abu.

17. Sai ya yi musu gargaɗi ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira masujadata ɗakin addu'a na dukkan al'ummai’? Amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”