Littafi Mai Tsarki

Luk 19:23-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. To, in haka ne, don me ba ka ajiye kuɗin nawa a banki ba, da dawowata in ƙarɓa, har da riba?”

24. Sai ya ce wa na tsaitsaye a wurin, ‘Ku karɓe fam ɗin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan.’

25. Suka ce masa, ‘Ya ubangiji, ai, yana da fam goma.’

26. ‘Ina dai gaya muku, duk mai abu a kan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai a karɓe masa.

27. Waɗannan maƙiya nawa kuwa, da ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ ”

28. Da Yesu ya faɗi haka, ya yi gaba zuwa Urushalima.

29. Da ya kusato Betafaji da Betanya, a wajen dutsen da ake kira Dutsen Zaitun, ya aiki almajiransa biyu,

30. ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi.

31. Kowa ya tambaye ku, ‘Don me kuke kwance shi?’ ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa.’ ”

32. Sai waɗanda aka aika suka tafi, suka tarar kamar yadda ya faɗa musu.

33. Suna cikin kwance aholakin, masu shi suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?”

34. Sai suka ce, “Ubangiji ne yake bukatarsa.”

35. Sai suka kawo shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa mayafansu a kan aholakin, suka ɗora Yesu.

36. Yana cikin tafiya, sai mutane suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya.