Littafi Mai Tsarki

Luk 19:12-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sai ya ce, “Wani mutum mai asali ya tafi wata ƙasa mai nisa neman sarauta yă dawo.

13. Sai ya kira bayinsa goma, ya ba su fam guda guda, ya kuma ce musu, ‘Ku yi ta jujjuya su har in dawo.’

14. Amma mutanensa suka ƙi shi, har suka aiki jakadu a bayansa, cewa ba sa so ya yi mulki a kansu.

15. Ana nan, da ya samo sarautar ya dawo, sai ya yi umarni a kirawo bayin nan da ya bai wa kuɗin, ya ga ribar da suka ci a wajen jujjuyawar.

16. Sai na farko ya zo gabansa, ya ce, ‘Ya ubangiji, fam ɗinka ya jawo fam goma.’

17. Sai shi kuma ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki! Tun da ka yi gaskiya a kan ƙaramin abu, to, na ba ka mulkin gari goma.’

18. Sai na biyun ya zo, ya ce, ‘Ya ubangida, fam ɗinka ya jawo fam biyar.’

19. Shi kuma ya ce masa, ‘Kai ma na ba ka mulkin gari biyar.’

20. Wani kuma ya zo, ya ce, ‘Ya ubangiji, ga fam ɗinka nan! Dā ma a mayani na ƙulle shi, na ajiye.

21. Domin ina tsoronka, don kai mutum ne mai tsanani, son banza a gare ka, kakan girbi abin da ba kai ka shuka ba.’

22. Sai ya ce masa ‘Kai mugun bawa! Zan yi maka shari'a bisa ga abin da ka faɗa da bakinka. Ashe, ka sani ni mutum ne mai tsanani, mai son banza, ina kuma girbar abin da ba ni na shuka ba?