Littafi Mai Tsarki

Luk 15:9-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. In kuwa ta same shi, sai ta tara ƙawayenta da maƙwabta mata, ta ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na sami kuɗin nan da na yar.’

10. Haka nake gaya muku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”

11. Ya kuma ce, “An yi wani mutum mai 'ya'ya biyu maza.

12. Sai ƙaramin ya ce wa ubansa, ‘Baba, ba ni rabona na gādo.’ Sai uban ya raba musu dukiyarsa.

13. Bayan 'yan kwanaki kaɗan sai ƙaramin ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa ƙasa mai nisa. A can ya fallasar da kayansa a wajen masha'a.

14. Da ya ɓad da kome kakat, aka yi babbar yunwa a ƙasar, sai ya shiga fatara.

15. Ya je ya rāɓu da wani ɗan ƙasar, shi kuwa ya tura shi makiyayar kiwon alade.

16. Har ma ya so ya cika cikinsa da kwasfar da aladu suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu

17. Amma da ya tara hankalinsa sai ya ce, ‘Kaitona! Nawa ne daga cikin barorin ubana da suke da abinci, da yake kamar ƙasa a gare su! Ga ni a nan kuwa, yunwa tana kisana!

18. Zan tashi, in tafi gun ubana, in ce masa, “Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka.

19. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin barorinka.” ’

20. Sai ya tashi, ya taho wurin ubansa. Amma tun yana daga nesa, sai ubansa ya hango shi, tausayi ya kama shi, ya yiwo gudu, ya rungume shi, ya yi ta sumbatarsa.

21. Sai kuma ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba.’