Littafi Mai Tsarki

L. Mah 15:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan 'yan kwanaki, sai Samson ya tafi ya ziyarci matarsa, ya kai mata ɗan akuya, a lokacin girbin alkama. Ya ce wa mahaifinta, “Zan shiga wurin matata a ɗakin kwana.”Amma mahaifinta bai yardar masa ba.

2. Ta ce wa Samson, “Na yi tsammani ba ka sonta ne sam, don haka sai na ba da ita ga wanda ya yi maka abokin ango. Amma ƙanwarta ta fi ta kyau. Ina roƙonka ka ɗauki ƙanwar maimakon matarka.”

3. Sai Samson ya ce musu, “A wannan lokaci, zan zama marar laifi saboda abin da zan yi wa Filistiyawa.”

4. Ya tafi ya kama yanyawa ɗari uku, ya haɗa wutsiyoyinsu, wato wutsiya da wutsiya, sa'an nan ya ɗaura jiniya tsakanin kowaɗanne wutsiya biyu.

5. Da ya sa wa jiniyar wuta, ya sake su zuwa cikin hatsin Filistiyawa. Suka ƙone dammunan hatsi, da hatsin da take a tsaye, da gonakin zaitun.

6. Filistiyawa kuwa suka ce, “Wane ne ya yi mana wannan abu?”Sai aka ce, “Samson ne, surukin mutumin Timna, domin ya ɗauki matar Samson ya ba wanda ya yi masa abokin ango.” Filistiyawa kuwa suka je suka ƙone matar, ta mutu, suka kuma ƙone gidan mahaifinta.

7. Samson ya ce musu, “Wato haka kuka yi! To, na rantse, ba zan bari ba sai na rama!”

8. Ya kuwa fāɗa musu, ya kashe su da yawa. Sa'an nan ya tafi ya zauna a kogon dutsen Itam.

9. Filistiyawa suka haura, suka kafa sansani a Yahudiya, suka bazu a cikin Lihai.