Littafi Mai Tsarki

Fit 39:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. An yi wa firistoci tufafi masu kyau na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, domin yin aiki a Wuri Mai Tsarki. Suka yi wa Haruna tsarkakan tufafi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

2. Ya yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

3. An kuma buga zinariya fake-fake, suka yanyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha.

4. Suka yi wa falmaran kafaɗu, sa'an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama.

5. Gwanin masaƙi ya saƙa abin ɗamarar falmaran. Da irin kayan da aka saƙa falmaran ne aka saƙa abin ɗamarar, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da zaren lallausan lilin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

6. Sai aka gyaggyarta duwatsu masu daraja aka jera su cikin tsaiko na zinariya. Aka zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi.