Littafi Mai Tsarki

Fit 37:14-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ƙawanen suna kusa da dajiyar inda za a zura sanduna na ɗaukar teburin.

15. Ya yi sanduna da itacen ƙirya don ɗaukar teburin. Sa'an nan ya dalaye su da zinariya.

16. Ya yi kayan teburin da zinariya tsantsa, wato farantansa, da kwanonin tuya, da kwanoninsa, da butoci domin yin hadaya ta sha.

17. Ya yi alkuki da zinariya tsantsa. An yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙunan alkukin da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da alkukin.

18. Akwai rassan fitila guda shida, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan.

19. A kowane reshe na alkukin akwai ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond, akwai kuma mahaɗai da furanni.

20. A bisa alkukin kuma akwai ƙoƙuna guda huɗu da aka yi su kamar tohon almond, da mahaɗai, da furanni.

21. Akwai mahaɗi kuma a ƙarƙashin kowane reshe biyu biyu na dukan rassan guda shida, a miƙe daga alkukin.

22. An ƙera mahaɗai da rassan alkuki a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi alkukin da dukan kome nasa a haɗe.

23. Da zinariya tsantsa ya yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa.

24. Da zinariya tsantsa na talanti ɗaya ya yi alkukin da kayayyakinsa duka.

25. Ya yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, shi murabba'i ne, tsayinsa kuma kamu biyu ne, zankayensa kuwa a haɗe suke da shi.

26. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, da bisansa, da kewayen gyaffansa, da zankayensa. Ya kewaye shi kuma da dajiya ta zinariya.