Littafi Mai Tsarki

Fit 2:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai wani mutum, Balawe, ya auro 'yar Lawi.

2. Matar kuwa ta yi ciki, ta haifi ɗa. Sa'ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har wata uku.

3. Da ta ga ba za ta iya ƙara ɓoye shi ba, sai ta saƙa kwando da iwa, ta yaɓe shi da katsi, ta sa jaririn a ciki, ta ajiye shi cikin kyauro a bakin Kogin Nilu.

4. Ga 'yar'uwarsa kuma a tsaye daga nesa don ta san abin da zai same shi.

5. Gimbiya, wato 'yar Fir'auna, ta gangaro domin ta yi wanka a Kogin Nilu, barorinta 'yan mata suna biye da ita a gaɓar Kogin Nilu. Da ta ga kwando a cikin kyauro, ta aiki baranyarta ta ɗauko mata shi.

6. Sa'ad da ta tuɗe kwandon ta ga jariri yana kuka. Sai ta ji tausayinsa, ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin 'ya'yan Ibraniyawa ne.”

7. 'Yar'uwar jaririn kuwa ta ce wa Gimbiya, “In tafi in kirawo miki wata daga cikin matan Ibraniyawa da za ta yi miki renon ɗan?”