Littafi Mai Tsarki

Fit 13:8-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. A wannan rana kowa zai sanar wa ɗansa cewa abubuwan nan da muke yi, muna yi ne don tunawa da abin da Ubangiji ya yi mana sa'ad da ya fitar da mu daga Masar.

9. Zai zama matuni kamar alama a hannunku, da abin tunawa a goshinku, domin shari'ar Ubangiji ta zama a bakinku, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fisshe ku daga Masar.

10. Sai ku kiyaye farillan nan kowace shekara a lokacinta.”

11. “Sa'ad da Ubangiji ya kai ku ƙasar Kan'aniyawa wadda zai ba ku kamar yadda ya rantse muku, ku da kakanninku,

12. sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Kowane ɗan farin dabbarku na Ubangiji ne.

13. Amma a fanshi kowane ɗan farin jakinku da ɗan rago. Idan kuwa ba za ku fanshe shi ba, sai ku karye wuyansa. Kowane ɗan farin 'ya'yanku, sai ku fanshe shi.

14. In wata rana 'ya'yanku suka tambaye ku cewa, ‘Ina ma'anar wannan?’ Sai ku ce musu, ‘Da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar, daga gidan bauta.

15. Gama sa'ad da Fir'auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, Ubangiji kuwa ya kashe dukan 'ya'yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba gaba ɗaya. Domin haka muke yin hadaya ga Ubangiji da 'ya'yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma mukan fanshi dukan 'ya'yan farinmu, maza.’

16. Al'amarin nan kuwa zai zama matuni kamar alama a hannunku ko a goshinku, gama da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar.”

17. Da Fir'auna ya bar jama'a su tafi, Allah bai bi da su ta hanyar ƙasar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ta fi kusa, gama Allah ya ce, “Don kada jama'a su sāke tunaninsu sa'ad da suka ga yaƙi, su koma Masar.”