Littafi Mai Tsarki

Fit 1:19-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Ungozomar suka ce wa Fir'auna, “Domin matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gama su masu ƙwazo ne, sukan haihu tun ungozomar ba su kai wurinsu ba.”

20. Allah kuwa ya yi wa ungozoman nan alheri. Mutanen suka riɓanya, suka ƙasaita ƙwarai.

21. Allah kuma ya ba ungozoman nan zuriya domin sun ji tsoronsa.

22. Fir'auna kuwa ya umarci dukan mutanensa ya ce, “Duk jaririn da aka haifa wa Ibraniyawa, sai ku jefa shi cikin Kogin Nilu, amma idan jaririya ce, ku bar ta da rai.”