Littafi Mai Tsarki

A.m. 25:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, da Festas ya iso lardinsa, bayan kwana uku sai ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima.

2. Sai manyan firistoci da manyan Yahudawa suka kai ƙarar Bulus gunsa, suka roƙe shi

3. ya kyauta musu, ya aika a zo da shi Urushalima, alhali kuwa sun shirya 'yan kwanto su kashe shi a hanya.

4. Amma Festas ya amsa ya ce, “Bulus yana a tsare a Kaisariya, ni ma kuwa da kaina ina niyyar zuwa can kwanan nan.”

5. Ya kuma ce, “Saboda haka, sai waɗansu manya a cikinku su taho tare da ni, in kuwa mutumin nan na da wani laifi, su yi ƙararsa.”

6. Bai fi kwana takwas ko goma a wurinsu ba, sai ya tafi Kaisariya. Kashegari kuma ya zauna a kan gadon shari'a, ya yi umarni a zo da Bulus.

7. Da ya zo, Yahudawan da suka zo daga Urushalima suka kewaye shi a tsaitsaye, suna ta kawo ƙararraki masu yawa masu tsanani a game da shi, waɗanda ma suka kasa tabbatarwa.

8. Amma Bulus ya kawo hanzarinsa ya ce, “Ni ban yi wani laifi game da shari'ar Yahudawa, ko Haikali, ko a game da Kaisar ba, ko kaɗan.”

9. Festas kuwa don neman farin jini wurin Yahudawa, ya amsa ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari'a a can a kan waɗannan abubuwa a gabana?”

10. Amma Bulus ya ce, “Ai, a tsaye nake a majalisar Kaisar, a inda ya kamata a yi mini shari'a. Ban yi wa Yahudawa wani laifi ba, kai kanka kuwa ka san da haka sarai.

11. To, in ni mai laifi ne, har na aikata abin da ya isa kisa, ai, ba zan guji a kashe ni ba, amma in ba wata gaskiya a cikin ƙarata da suke yi, to, ba mai iya bashe ni gare su don a faranta musu rai. Na nema a ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar.”

12. Bayan da Festas ya yi shawara da majalisa, sai ya amsa ya ce, “To, ka nema a ɗaukaka ƙararka gaban Kaisar! Gun Kaisar kuwa za ka tafi.”

13. Bayan 'yan kwanaki sai sarki Agaribas da Barniki, suka zo Kaisariya don su yi wa Festas maraba.