Littafi Mai Tsarki

A.m. 21:8-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Kashegari muka tashi muka zo Kaisariya, muka shiga gidan Filibus mai yin bishara, wanda yake ɗaya daga cikin bakwai ɗin nan, muka sauka a wurinsa.

9. Shi kuwa yana da 'ya'ya huɗu 'yan mata, masu yin annabci.

10. To, muna nan zaune 'yan kwanaki, sai wani annabi, mai suna Agabas, ya zo daga Yahudiya.

11. Da ya zo gare mu, ya ɗauki ɗamarar Bulus ya ɗaure kansa sawu da hannu, ya ce, “Ga abin da Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara, su kuma bashe shi ga al'ummai.’ ”

12. Da muka ji haka, mu da waɗanda suke wurin muka roƙi Bulus kada ya je Urushalima.

13. Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me ke nan kuke yi, kuna kuka kuna baƙanta mini rai? Ai, ni a shirye nake, ba wai a ɗaure ni kawai ba, har ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”

14. Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Ubangiji ya yi yadda ya so.”

15. Bayan 'yan kwanakin nan muka shirya muka tafi Urushalima.

16. Waɗansu masu bi daga Kaisariya suka rako mu, suka kawo mu wurin Manason, mutumin Kubrus, wani daɗaɗɗen mai bi, wanda za mu sauka a gunsa.

17. Da muka zo Urushalima, 'yan'uwa suka karɓe mu da murna.

18. Kashegari Bulus ya tafi tare da mu wurin Yakubu, dattawan Ikkilisiya kuwa duk suna nan.

19. Bayan da ya gaisa da su, sai ya shiga bayyana musu filla filla abubuwan da Allah ya yi a cikin al'ummai ta wurin hidimarsa.

20. Su kuwa da suka ji haka, suka ɗaukaka Allah. Suka ce wa Bulus, “To, kā gani ɗan'uwa, dubban mutane sun ba da gaskiya a cikin Yahudawa, dukansu kuwa masu himma ne wajen bin Shari'a.

21. An kuwa sha gaya musu labarinka, cewa kai ne kake koya wa dukan Yahudawan da suke cikin al'ummai su yar da Shari'ar Musa. Wai kuma kana ce musu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya, ko kuwa su bi al'adu.

22. To, ƙaƙa ke nan? Lalle za su ji labarin zuwanka.

23. Saboda haka sai ka yi abin da za mu faɗa maka. Muna da mutum huɗu da suka ɗauki wa'adi.

24. Sai ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka, kowa zai sani duk abin da aka gaya musu game da kai, ba wata gaskiya a ciki, kai kuma kana kiyaye Shari'a.